Revelation of John 16

1Na ji babban murya na kira daga cikin haikali tana ce wa malai’iku bakwai, ‘’Ku je ku zuba tasoshi bakwai na fushin Allah a kan duniya.”

2Mala’ika na fari ya je ya zuba tasarsa a kan duniya; munanan gyambuna masu zafi suka fito wa mutane wadanda suke da alamar dabbar, wadanda suka bauta wa siffarsa.

3Mala’ika na biyu ya zuba tasarsa cikin teku. Ya zama jini, kamar jinin wanda ya mutu, kuma kowane abu mai rai da ke cikin tekun ya mutu.’

4Malaika na uku ya zuba tasarsa a cikin rafuffuka da mabulbulan ruwa, sai suka zama jini. 5Na ji mala’ikan ruwaye ya ce, ‘’Kai mai adalci ne - wanda ya ke yanzu wanda yake kuma a da, Mai Tsarkin nan, domin ka shari’anta wadannan abubuwa. 6Domin sun zubar da jinin masu ba da gaskiya da annabawa, ka basu jini su sha; shine abinda da ya dace da su. 7Na ji bagadi ya amsa, ‘’I, Ubangiji Allah Mai iko duka, shari’un ka gaskiya ne da adalci.‘’

8Mala’ika na hudu ya zuba tasarsa a kan rana, kuma aka ba shi izini ya kone jama’a da wuta. 9Suka kone da zafi mai tsanani, kuma suka sabi sunan Allah, wanda ke da iko akan annobai. Ba su tuba ba ko su daukaka shi.

10Sai malaika na biyar ya zuba tasarsa a kan kursiyin dabban, sai duhu ya rufe mulkinsa. Suka cicciji harsunansu saboda zafi. 11Suka yi sabon Allah na sama domin zafi da gyambunansu, suka kuma ki su tuba daga abin da suka yi.

12Mala’ika na shida ya zuba tasarsa cikin babban rafi, Yufiretis. Ruwansa ya bushe domin a shirya hanya da sarakuna za su zo daga gabas. 13Na ga kazamun ruhohi uku suna kama da kwadin da ke fitowa daga bakin diragon, da makaryacin annabi. 14Gama su ruhohin aljanu ne masu aikata alamun ban mamaki. Sun fita za su wurin sarakunan dukan duniya domin su tattaro su wuri daya saboda yaki a babbar ranar Allah Mai iko duka.

15(‘’Duba! Ina zuwa kamar barawo! Mai albarka ne wanda ke zaune a fadake, wanda ke sanye da tufafinsa domin ba zai fita tsirara a ga tsiraicin sa ba.”) 16Aka kawo su tare a wurin da ake kira Armagiddon da Ibraniyanci.

17Mala’ika na bakwai ya zuba tasarsa cikin iska. Sa’annan babbar murya ta fito daga cikin haikali da kuma kursiyin, cewa, ‘’An gama!‘’ 18Aka yi walkiya, da kararraki masu tsanani, da aradu da babbar girgizar kasa - girgizar da ta fi kowacce da aka taba yi tun da ‘yan adam suke a duniya, girgizar da girma ta ke. 19Babban birnin ya rabu kashi uku, kuma biranen al’ummai suka fadi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, sai ya ba wancan birnin koko cike da ruwan innabi wanda aka yi daga fushinsa mai tsanani.

20Kowanne tsibiri ya bace, sai ba a kara ganin duwatsun ba. Manyan duwatsun kankara, masu nauyin talanti, suka fado daga sama kan mutane. Suka zagi Allah domin annobar kankarar saboda annobar ta yi tsanani.

21

Copyright information for HauULB